Kada kayi missing Ιin wannan post Ιin zai iya chanja maka tunani
Idan ba zaka raina kaΙan ba, tou ba zaka taΙa rasa opportunity ba.
Wani so yake dole sai first gig Ιin shi ya samu $1K, kamar yadda yaga
@Yusi0x,
@Uthmankhan_,
@CreativityEngr suke samu.
Kaicon ka, Ιan baiwa... Bai san suma ba, ranar da suka fara Web3 suka fara samun $1K ba.
It's a long TIME JOURNEY. Idan kayi haΖuri da kaΙan mai albarka, sai ka samu $1K ba tare da wata wahala ba.
Amma mutanen mu akwai su da raina kaΙan.
A
@TrustChain0 Academy, student suna nan suna winning, duk da mutane suna ganin cewa babu aiki!
Shin ko babu aiki a Web3?
@Yusi0x yayi wani posting a kwanakin baya yana cewa, ganda tare da rashin research da rashin exploring yasa mutane suna ganin cewa babu aiki a Web3.
Tabbas akwai opportunities a Web3. Wallahi rashin bincike da exploring yasa bama samun su.
Wani ya raina wata Ζ΄an $5 ko $10, shi kawai $100 shine minimum gig Ιinda yake chasing. Bro, Shine your Eyes, is better you should get $10 than to sit down, notin dey in your pocket.
Idan kaji wani OG yace ba zai karΙi aikin $50 ba ko $100, tou ka sani cewa, "kowace tsintuwa da mai Ιaukar ta."
Bari na fito maka da karatun a fili.
Idan Ζaramin yaro ya tsinci β¦10, zai kama jin Ιadi yana celebrating ba?
Kai kuma, ko kallo bata isheka ba, domin ko Pure water ba zata saya maka, depending a gurin da kake rayuwa.
Ina fatar karatun ya fita fes-fes? To, madalla!
Dabara ta rage ga mai shiga rijiya, inji Malam bahaushe!
Ko dai Ιan baiwa yayi karatu, ya nemi SKILLS, yana kama research, yana samun na biyan bukatun sa.
Ko kuma jiki magayi. NAJERIYA kake, baka buΖatar motivation.
Allah yasa mu wanye lafiya! Na barku lafiya.