Ya Allah nasan ba lallai ne Sallah da Addu’ar da nake yi yayi dai dai yadda kake so ayi ba,
ya Allah nasan bana yin azumi kamar yadda Annabin ka Annabi Dauda Alaihissalam yake yi
Nasan idan banda lafiya, bana iya hakuri kamar yadda Annabi ayyuba yayi.
Kuma idan raina abace, bana iya tasbihi kamar annabi Yunus Alaihissalam yakeyi.
Ya rabb nasan bazan iya yin sadaukarwar da sukayi, Ya Allah nasan gare ka ne kadai ake samun yanci.
Ya Rabb ni mai kaunar ka ne, Ya Aallah ni mai yi maka biyayya ne, ya Allah ni mabiyn manzon ka SAW masoyin sa kuma mai masa biyayyah ne.
Ya rabbi kaine kake jarraba bayinka yadda kaso, mulkinkane, ikon kane, Yarabbi kayayemana damuwarmu kasauqaqa mana domin kaine mai saukakawa,
gareka muke neman taimako yarabbi karka barmu da kanmu koda da qibtawar idone ,Allah ka musanya mana farinciki lallai kaine maijuya damuwa zuwa walwala 🥹🙏