> Me Ake Nufi Da: Memory Forensics (RAM Analysis)
> Memory Forensics Ko Kace RAM Analysis Wata Hanya Ce Ta Binciken Dijital Da Ake Amfani Da Ita Wajen Nazarin Bayanai Da Suke Cikin RAM (Random Access Memory) Na Kwamfuta Ko Wata Na'ura A Lokacin Da Take Aiki.
> RAM Shine Ƙwaƙwalwar Ajiya Ta Ɗan Lokaci Da Kwamfuta Ke Amfani Da Ita Yayin Gudanar Da Ayyuka Daban Daban, Acikin RAM Ana Iya Samun Running Processes, Open Applications, Network Connections, User Sessions, Da Sauran Muhimman Bayanai Da Ke Gudana A Wannan Lokacin.
> Ɗaya Daga Cikin Muhimman Dalilan Da Suka Sa Memory Forensics Ke Da Matuƙar Muhimmanci Shine Saboda Wasu Bayanai Ba Sa Tsayawa A Hard Disk, Da Zarar An Kashe Na'ura, Yawancin Abubuwan Da Ke Cikin RAM Suna Bacewa, Wanda Ke Sa Ta Zama Wata Muhimmiya Wajen Tattara Shaidu Kafin Su Ɓace.
> Ta Hanyar Memory Forensics, Ana Iya Gano Active Processes Da Suke Aiki, Network Connections Da Aka Buɗe, User Activities, Da Kuma Wasu Nau'ikan Malware Da Suke Aiki A Boye Ba Tare Da Sun Rubuta Bayanan Kansu A Hard Disk Ba.
> Haka Kuma Ana Iya Gano Wasu Muhimman Bayanai Kamar Open Files, Browser Sessions, Da Wani Lokaci Har Ma Encryption Keys Da Ke Taimakawa Masu Bincike Fahimtar Yadda Wani Hari Ko Matsala Ta Faru.
> Aikin Memory Forensics Yana Farawa Ne Da Ɗaukar Cikakken Kwafin RAM Wanda Ake Kira Memory Dump, Sannan A Yi Nazari A Kai Ta Amfani Da Kayan Aiki Kamar FTK Imager Wannan Daliban Mu Sunsan Ya Ake Aiki Dashi, Sai Kuma DumpIt, WinPmem Da Volatility.
> Wannan Fanni Yana Da Muhimmanci Sosai A Incident Response, Malware Analysis, Threat Hunting, Da Digital Forensics Saboda Yana Taimakawa Masana Tsaro Su Gano Abubuwan Da Ke Faruwa Kai Tsaye A Cikin Tsari.
#Cybersecurity #MemoryForensics #RAMAnalysis