YADDA ZAKA FARA SAMUN KUƊI DA AIKIN COLLAB MANAGER - Part 1
As promised yesterday, Collaboration Manager (Collab Manager) yana daga cikin roles masu sauki a Web3, domin ya banbanta da sauran Roles wanda zaka zauna tsawon lokaci ka koyi skills nasu Sannan ka fara Fafutukar samun aiki dasu,
Collab Manager aikin shi ba wani mai tsawo bane, hakan yasa ko kanada Followers ko babu, ko kana da experience ko babu, indai kana da ilimin fundamental analysis zaka iya.
Like Retweet and Bookmark 🔖
Wane ne Collab Manager?
Collab Manager shine mutumin dayake zuwa yayi bincike ya samo project da suke buƙatar masu aiki, sai ya haɗa su da Ma'aikatan da suke buƙata.
Wato kamar ace Ɗan tsakiya ne (MiddleMan).
Aikinsa yaje ya binciko project da suke buƙatar kalar ma'aikatan dayasan zai iya reaching dinsu, sai ya haɗa su da project suyi musu aiki shi kuma su bashi Percentage dinsa. That's Collaboration Manager.
Tayaya zaka fara?
Ta hanyar Farawa da sanin Abinda zaka dinga Nunawa project da kuma waɗanda zaka nemo project ɗin ka haɗa su da su, Misali; zaka samo KOLs/Ambs etc…. Su waye suke da wannan role? Misali kamar Ni ko
@Yusi0x,
@Uthmankhan0 ,
@aliy_almustapha da sauran wasu da dama.
Kowanne Acikin Mu KOL ne kuma Ambassador, sedai akwai tiers.
Sai ka kaje kayi bincike ka samo project da suke buƙatar Promotion, wato a tallata musu Product dinsu.
Taya zaka samo su?
Ta hanyar zuwa DMs dinsu ko kai tsaye zuwa ga Founders nasu, Ka Nuna musu cewar kana da Wasu Kwararru da zasu iya promoting/pushing din Project din nasu.
Idan akaci Sa'a suka saurare ka, suka nuna suna bukatar Aikin, To anan kuma sai kaje kayi reaching Yusi ko wani daga Cikin mu da maganar, Sai kuyi Agreement dashi akan irin % din da zai baka idan har akaci nasara deal din ya ƙullu, Misali ace 10% za'a baka. Means idan aikin da za'a musu zasu biya $1000, that's $100 kake da for a single successful deal.
Wannan shine yadda Aikin Collab Manager yake, idan kana da Sa'a da Nasibi acikin sati zaka iya qulla deal 1–3 zuwa sama, imagine you got 3 deals and all went successfully, kaga zaka tashi da kuɗi masu kyau.
Wannan misali ne akan iya aikin Promotion na bayar, amma duka haka Ragowar ayyukan suke, graphic designer, community builder, Dev and more. Kowanne zaka iya kai musu aiki a qulla deal ka samu Percentage dinka.
Mai yiwuwa Su basada Lokacin tafiya Nemo projects din, amma idan aiki ya samu zasuyi, To kaga anan ne kai kuma Damar ka ta samu.
Saboda haka wannan aikin ba mai wahala bane kamar saura, what you need all is to have enough knowledge to research and reach
a good Projects.
Idan hali yayi a gaba zan kawo muku sample Dm messages da zaku dinga turawa domin samun reply da wuri wanda muke kira da (pitching)
If you found it helpful
👉 follow
@CreativityEngr to get more and more about Web3!
👉 Like and Retweet for others.
👉 Check profile for older lessons You Missed!
#collabmanager #Web3