Ahmad XM Na Gina Blockchain Estate Da Zaku Iya Sayan Gida A Ciki Da Crypto 💁
Shahararren mai harkar kudaden intanet (Crypto), Ahmad XM, ya bayyana wani gagarumin shiri da yake gudanarwa na gina wani katafaren rukunin gidaje da ya sanya wa suna "Blockchain Estate
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmad XM ya sanar da cewa wannan rukunin gidaje zai zo da wani sabon salo na daban wanda ba a saba gani ba a fannin gine-gine. Maimakon amfani da lambobi (numbers) wajen alamta gidaje kamar yadda aka saba, a wannan Estate din, kowane gida zai amsa sunan daya daga cikin shahararrun kudaden crypto. Wannan yana nufin ana iya kiran gidajen da sunaye irin su Bitcoin, Ethereum, Solana, da sauran su.
Wani babban abin burgewa da ya jawo hankalin mutane shi ne sanarwar da ya yi cewa za a iya sayen wadannan gidaje ta hanyar amfani da kudaden crypto. Wannan na nufin duk mai bukatar mallakar gida a rukunin na Blockchain Estate, ba sai ya yi amfani da takardun kudi na Naira ko Dala ba; zai iya biyan kudin gidan kai-tsaye ta walat dinsa ta crypto.
Ana ganin cewa wannan mataki zai zama babbar dama ga matasa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar crypto domin mallakar gidaje na kece-raini. Idan aka kammala aikin wannan Estate, ana sa ran zai zama wurin alfahari ga daukacin masu harkar fasahar blockchain, ganin yadda aka tsara shi domin ya yi daidai da rayuwar zamani ta dijital.
Wannan yunkuri na Ahmad XM ya sake tabbatar da yadda fasahar blockchain take kara shiga cikin sauran sassan rayuwar al'umma, ba wai kawai a fannin kudi ba, har ma da fannin mallakar gidaje da filaye
@ahmedxm01 🤝