Rashin Tsaro: Shin Mun Gaza Fiye da Zamanin Jahiliyya?
Abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan dangane da rashin tsaro sun wuce misali. Shin haka za mu cigaba da zaman kamar ba mu da shugabanni, babu sarakuna, babu malamai, kuma babu dattawa?
Sau da yawa nakan ce, ko a zamanin dauri ba haka ƙasar Hausa take ba. Muna da tsare-tsaren tsaro masu ƙarfi da suka dace da lokacin, waɗanda suka iya magance irin matsalolin da muke fuskanta a yau.
Mene ne amfanin tsarin mulkin zamani idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin al'umma ba?
Ba tare da wata shakka ba, mun kai wani matsayi da ya fi na jahiliyya muni. A wancan lokaci, ƙabila kan ɗauki shekaru tana neman adalci ko ɗaukar fansa saboda an kashe mata mutum ɗaya ko an sace matar wani. A yau kuwa, ba ma iya kare kanmu.
Yanzu labarin kashe wani babban hafsan soja ya zama tamkar wani al'amari na yau da kullum. Ballantana kuma ɗan sanda, wanda kimarsa ta ragu matuƙa a idanun jama'a.
A da, idan aka rasa ko soja guda ɗaya a fagen fama, sai an gudanar da bincike mai zurfi. Kwamandoji kan fuskanci tambayoyi masu zafi, kuma wani lokaci har a cire su daga muƙamansu. Amma a yau, ana kashe manyan hafsoshin soja a Najeriya a cigaba da rayuwa kamar an kashe karnuka.
Tun daga shekarar da ta gabata zuwa yau, janar-janar nawa aka kashe?
Daga ranar da kashe soja ya zama kamar ba komai ba, to kashe farar hula ya zama abu mafi sauƙi. Domin idan masu ɗauke da makamai da kare ƙasa ba su da kariya, me zai hana marasa galihu su zama ganima?
A zahiri, sojoji ne kaɗai suka rage da wani ɗan mutunci a cikin hukumomin ƙasar nan, saboda tsarin biyayya da bin doka da suke aiki da shi. Amma duk da haka, su ma ba su tsira daga wannan bala'i ba.
Yanzu haka kusan babu ranar da za mu wayi gari ba tare da jin labarin kashe-kashe, satar mutane, da lalata dukiyoyi ba. Ana kashe mutane a gidajensu, a gonakinsu, da wuraren neman abincinsu.
Shin da gaske muna son mu ce ba mu san waɗanda ke aikata waɗannan laifuka ba?
Ƙarya ce. Abin da ke damunmu shi ne tsoro.
Idan ka tattauna da mutanen ƙauyukan da wannan matsala ta fi shafa, za ka fahimci cewa suna sane da waɗanda ke aikata waɗannan muggan ayyuka. Wasu daga cikinsu ma sun taɓa rayuwa tare da su a baya.
Sun san su, sun san asalinsu, kuma suna da masaniya kan wuraren da suke kafa sansaninsu.
A lokacin da ake ganin ba mu da wayewar zamani, sarkin daji ya san kowane lungu da saƙo na dazuzzukan da ke ƙarƙashin kulawarsa. Akwai mahayan dawakai da aikinsu shi ne sintiri domin gano duk wani abu da ba a saba gani ba.
To me ya sa a ƙarni na ashirin da ɗaya muka kasa yin abin da kakanninmu suka iya yi da ƙarancin kayan aiki?
Abin kunya ne, kuma abin takaici ne ganin yadda muke rasa rayukan mutanen kirki masu hangen nesa.
Wannan ci gaban da muke taƙama da shi, shi ne irin wanda Bahaushe ke kira "ci gaban mai haƙar rijiya." Ci gaba a suna, koma baya a aikace.
Duk da haka, har yanzu ba mu makara ba.
Idan shugabannin gargajiya da malamai da dattawa, da sauran masu ruwa da tsaki suka haɗa kai da gaske, za a iya samar da zaman lafiya da ya dace da zamanin da muke ciki.
Mataki na farko wajen magance kowace matsala shi ne fahimtar matsalar da kuma waɗanda ke haddasa ta. Na yi imani cewa waɗannan bayanai suna nan, kuma akwai waɗanda suka san abin da ke faruwa da kuma hanyoyin magance su.
Abin da ya rage shi ne ƙarfin hali da niyyar ɗaukar mataki.
© Zaharaddeen Ibrahim Kallah