Elon Musk Ya Kama Hanyar Zama Trillionaire Na Farko A Duniya...
Yau ake saran za'ayi IPO na Space X, babban kamfanin nan na Elon Musk, hakan na nufin kamfanin zai fara sayar da hannun jarinsa ga jama'a a kasuwar hada-hadar hannayen jari.
IPO (Initial Public Offering) shi ne matakin da kamfani ke fita daga kasancewa na masu zaman kansu (private) zuwa kamfanin da kowa zai iya sayen hannun jarinsa.
Kafin yau, ba za ka iya siyan hannun jarin SpaceX kai tsaye kamar yadda ake siyan na Tesla, Apple ko Microsoft ba, domin SpaceX kamfani ne mai zaman kansa (private). Amma yau zai zama kamfani na kowa da kowa.
Yau da SpaceX zata shiga fagen IPO, miliyoyin masu zuba jari a duniya za su samu damar mallakar wani bangare na wannan babban kamfanin sararin samaniya na Elon Musk.
Ana hasashen valuation na kamfanin Elon Musk ɗin za'a fara trading ɗin sa akan $2 trillion 🙆.
Muna gefe a dex mun ci kasuwar trend ɗin, muna kuma jiran IPO na matatar Man Ɗangote anan kusa In shaa Allahu. Idan wannan ya fito, ko N100,000 ce ka siyawa Ƴaƴanka, in da rabo a gaba su amfana. Amma na Elon Musk yayi mini nauyi da yawa.