Menene Sharding?
Sharding wata dabara ce a fasahar blockchain da ake amfani da ita domin ƙara saurin aiki da girman (scalability) ta hanyar raba network zuwa ƙananan sassa da ake kira shards. Kowanne shard yana iya sarrafa transactions (mu’amaloli) da kansa.Sharding asali daga database ya fito. A databases, ana raba bayanai masu yawa zuwa sassa daban-daban a kan hardware daban-daban domin ajiya ya fi tsaro, sauƙin sarrafawa, da dacewa da kayan aiki.A Ethereum 2.0, da farko an tsara 64 shards domin raba bayanan blockchain. Amma bayan The Merge da Dencun upgrade, Ethereum ya juya zuwa rollup-centric roadmap tare da Danksharding. A yanzu babban abin da yake mai da hankali shine data availability (DA) don Layer 2 rollups.Danksharding shine sabon tsari wanda ke ba da babban adadin blobs (manyan data packets) a kowane block. Manufarsa ita ce rage farashin data posting ga rollups sosai, ta yadda za a iya samun sama da 100,000 TPS (transactions per second) a duk tsarin Ethereum (musamman ta hanyar L2s) a nan gaba.Proto-Danksharding (EIP-4844) an aiwatar da shi a Dencun upgrade a Maris 2024. Shi ne mataki na wucin gadi da ake amfani dashi yanzu a hanyar zuwa full Danksharding. Manufarsa ita ce rage farashin mu’amaloli a kan Layer 2 yadda zai yi sauƙi sosai ga masu amfani.
#CryptoEducation
#LearnBlockchain