Shin kana fama da matsalar kuɗi? To ga wasu muhimman shawarwari... Mutane da dama ba sa gane muhimmancin tsara rayuwar kuɗi da tattalin arzikinsu sai bayan lokaci ya kure musu. Za ka ga matsahi ya yi digiri, ya samu aiki, sai ya tara ‘yan kuɗi kaɗan, sai ya hada lefe, ya kama gida, ya yi aure, ya haifi yara. Sai ƙarin haihuwa. Bayan shekara biyar ko goma, iyali sun ƙaru, buƙatu sun yawaita, kuma ga shi kuɗin shiga bai ƙaru ba, amma farashi kuma sai ci gaba da tashin gwauron zabo yake yi. Daga nan, sai ka ji babu isasshen abinci, babu tufafi, babu kuɗin makaranta, babu...babu... — sai bashi da matsin tattalin arziƙi.
Wato yadda abun yake shi ne, kana kara girma, kana buƙatar ƙarin kuɗin shiga, da ƙarin hanyoyin samun kuɗi, da ƙarin alert alert. Saboda kana kara shekaru kana kara samun nauyin kuɗin sayan magani, da kuɗin makaranta, da na abinci, da sauran bukatun iyali, da kula da iyaye da suka girma, ha ƙarin yara, ga kuma tashin farashi. Shi ya sa dole ka fara tattali da tanadi da ajiya da saka hannun jari da Kasuwanci tun yau. Idan ka fara tun daga yau, ka gara da wuri, to gobe za ka samu ƙarin kuɗin shiga kuma ka rayu cikin walwala da daukin rayuwa, Insha Allah.
Dan’uwa, ka tsara rayuwarka. Ka tsara makomarka. Ka tsara iliminka. Ka tsara addininka. Ka tsara makomar iyalinka. Ka tsara lahirarka. Ka tsara harkokin kuɗinka. Rayuwa tana buƙatar tsari. Kada ka rayu kara-zube ba tare da manufa da tsari ba.
Abokina, maza je ka fara koyon ilimin neman kuɗi da sarrafa su da bunkasa su da tattala su. Ka koyi ilimin kudi, ka tsara nemansu, ka neme su, ka ƙara nema, ka yi ajiya, ka tara su, ka habaka su ka saka jari, ka sake saka jari, sannan ka dage da aiki domin inganta rayuwar tattalin arziƙinka, bisa doron shari'ah, Insha Allah.
Ba a fafe gora ranar tafiya. Saboda haka: ka koya, ka tsara, ka aiwatar, kuma ka yi addu’a. Sannan, ka kasance mai jajircewa da juriya.
- Amir Lamido